Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe sun ceto Aishatu Mohammed ‘yar shekara 4 daga hannun masu garkuwa da mutane.
‘Yan sandan SARS sun gurfanar da wadanda ake zargi da garkuwar, mai suna Hadiza Babayo, 18, da wani mai suna Bala Shuaibu a ranar Juma’a a Gombe.
A yayin gurfanar da su, Kakakin ‘yan sandan SP Mary Malum, ta tabbatar da cewa; jami’an SARS din sun kama wadanda ake zargi ne bayan sun samu bayanan sirri, inda suka kama Babayo a karamar hukumar Lafiya da kuma Bala daga karamar hukumar Lamurde.
Ta tabbatar da cewa; a yayin gudanar da binciken, Babayo ta amsa laifinta. Inda ta bayyana yadda ita da wani mai suna Bala Shuaibu suka sace yarinyar daga wata makaranta suka ajiye ta a wani otel dake Nayi-Nawa kwatas a Gombe, inda suka nemi a biya naira miliyan 6 a matsayin kudin fansa kafin a sake yarinyar.
Inda ta ce bayan jami’an SARS sum samu labari, shi ne suka je suka ceto yarinyar kafin a kai ga biyan kudin fansar.
Kawun yarinyar, Alh. Umar Shafudeen, wanda ya zanta da majiyarmu, ya ce sun matukar kaduwa cikin awa 24 da sace yarinyar. Ya ce bayan sun samu labarin sace yarinyar ne, suka shidawa Kwamishinan ‘yan sanda, shi kuma ya aika jami’ansa suka ‘yanto yarinyar.