By Abbas Yakubu Yaura
An dage zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Oyo.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito idan zaku iya tuna cewa a yau Alhamis ne aka shirya gudanar da zaben fidda gwanin.
Ana sa ran za a yi shi a filin wasa na Obafemi Awolowo, dake Oke Ado Ibadan.
‘Yan takara shida wadanda dukkaninsu ‘yan asalin Ibadan ne, babban birnin jihar sun fito don fafatawa ne domin samun tikitin tsayawa takarar jam’iyyar gabanin babban zaben 2023.
‘Yan takarar shida sun hada da Sanata mai wakiltar mazabar Oyo ta tsakiya, Teslim Folarin, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Cif Adebayo Adelabu, babban lauyan Najeriya (SAN) Cif Adeniyi Akintola, tsohon kwamishinan lafiya, Dr.Azeez Adeduntan, da Barista Akeem Agbaje da kuma Injiniya Oyedele Hakeem Alao.
Wakilinmu da ke wurin ya tattaro cewa an dage zaben fidda gwani, duk da cewa ba a bayyana shi a hukumance ba.
Yayin da wasu ke cewa an dage zaben fidda gwani har sai abinda hali yayi, wasu kuma na da ra’ayin cewa za a gudanar da zaben fidda gwani a gobe Juma’a.
Wakilinmu ya ruwaito cewa an dage zaben fidda gwani da za a yi a ranar Alhamis da yamma bayan Shugaban kwamitin zaben Sanata Tokunbo Afikuyomi da Kwamishinan Zabe na Jihar Barista Mutiu Agboke da ‘yan takarar suka iso filin zaben.
Wadanda aka gani a wurin taron sun hada da Folarin, Adelabu, Adeduntan, Agbaje da Alao.
Duk kokarin da ‘yan jaridan da suka je wurin domin sanin babban dalilin dage zaben ya ci tura, duk da cewa wasu majiyoyin da suka yi magana cikin aminci sun bayyana cewa an dage zaben ne saboda kalubalen tsaro.
Jita-jitar dage zaben ta fara fitowa fili ne a lokacin da Afikuyomi, Agboke, masu neman tsayawa takara da jami’an tsaro ke barin wurin taron.
Hakan ya sanya ‘yan jaridan da suka dade suna jiran lokacin fara zaben fidda gwanin suma suka bar wurin.
Comments 1