By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon dan majalisa mai wakiltar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye, ya rasa tikitin tsayawa takara na jam’iyyar PDP a hannun wani dan majalisar wakilai mai ci, Hon. Yusuf T.J.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an tafka zazzafar muhawara a zaben fidda gwani na Sanatan PDP na Kogi ta Yamma inda Dino Melaye ya samu kuri’u 88 yayin da TJ Yusuf ya samu kuri’u 88 wanda ya kai ga sake zaben ranar Talata.
A zaben da aka sake gudanarwa ranar Talata, Hon. T. J. Yusuf ya doke Sanata Dino Melaye da kuri’u 163 yayin da Dino ya samu 99 inda ya samu tikitin takarar PDP.
Yusuf, a lokacin da yake magana bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, ya mika reshen zaitun ga abokan takararsa, inda ya bukaci su hada kai da shi domin lashe babban zaben.
Ya yaba da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani cikin kwanciyar hankali, inda ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukansa nagari idan har aka zabe shi a babban zabe.
A wani labarin kuma Air Vice Marshal Napoleon Bali (Mai ritaya) ya lashe zaben fidda gwani na babbar jam’iyyar adawa ta kasa PDP na tikitin takarar Sanatan Filatu ta Kudu a zaben shekarar 2023.
Bali wanda ya taba rike mukamin Shugaban tsare tsare a shalkwatar rundunar sojin sama ta kasa(COPP) HQ NAF, ya samu kuri’u 141 inda ya kayar da tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Johnbull Shekarau, wanda ya samu kuri’u 61 a kuri’un da aka kada a zaben.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa Bali zai fafata da Gwamna Simon Lalong wanda shi ne dan takarar jam’iyyar All APC mai mulki.
Comments 1