Daga Jihar Lagos Zuwa Jihar Borno Maiduguri, sune Jihohi mafi tsawo a tsakanin Najeriya har masana sun ce a kallah zai kai Kilomita 1300 a tsakani Lagos zuwa Borno.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na ziyara a jihar Legas domin kaddamar da wasu ayyukan da Gwamnan jihar mai barin gado ya yi, kafin ya wuce Borno a gobe Alhamis kamar yadda wata majiya daga fadar shugaban kasar ta sanar.
Ayyukan da shugaban zai kaddamar sun hada da bude Cibiyar Kula da Lafiyar Uwa da Da, da hanyar sufurin motoci da ke unguwar Oshodi da kuma hanyar filin jiragen sama na kasa da kasa, yayinda kuma zai kaddamar da sabbin motoci 820 na jigilar fasinjoji.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar Tuni aka girke jami’an tsaro musamman a wuraren da shugaban zai ziyarta a Lagos kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran kasar wato NAN ya rawaito
Jami’an sun hada da Sojin Sama da Kwastam da Jami’an Kula da Shige da Fice da Jami’an Tsaron Farin kaya da kuma Jami’an Kiyaye Hadduran Ababawan Hawa.
Ana saran shugaba Buhari ya ziyarci jihar Katsina a cikin mako mai zuwa, in da zai shafe mako daya kamar yadda majiya daga fadarsa ta sanar.