By Abbas Yakubu Yaura
Oluwo na Iwo land, Oba Abdularosheed Adewale Akanbi (Telu 1) ya auri gimbiyar sa a Kano,mai suna Firdaus Abdullahi, wacce takasance jikar marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ce.
Daurin auren wanda ya gudana a gidan Madakin Kano,a ranar 19 ga watan Maris ba a samu fitowar manyan baki ba duk da cewa ma’auratan sun fito ne daga gidan sarauta.
DUBA WANNAN LABARIN: Mutane Bakwai Sun Jikkata Yayin Wani Rikicin Magoya Bayan Jam’iyya Da ‘Yan Sanda A Guinea-bissau
Daurin auren ya samu halartar wakilin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Sanata Babafemi Ojudu, wanda shi ne mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin siyasa; Sarkin Yarbawa na Kano da Sarkin ’Yarbawa na Zazzau, a tsakanin wasu manyan sarakunan sarauta.
An biya kudin sadaki naira miliyan daya ga amaryar wanda wakilan angon suka bayar da tsabar kudi a gaban Madakin Kano na yanzu Yusuf Ibrahim Cigari.
Amaryar wacce diyar marigayi Madakin Kano ce, Alhaji Abdullahi Sarki Sani Yola, tsohon magatakardar majalisar dokokin jihar Alhaji Mahmood Sani ne ya baiwa ango auren ta , yayin da Babalaji na Iwo land Barista Ismail Oteyeku ya wakilci majalisar angon ya kuma karba masa aurenta.
Firdaus, wacce ‘yar uwa ce ga Sarkin Kano na yanzu, Alhaji Aminu Ado Bayero, ta yi karatun difloma a fannin abinci daga Kwalejin fasaha ta Kano.
Ta taba yin aure amma mijinta ya rasu.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan daurin auren, wakilin angon ya ce daya daga cikin makasudin daurin auren shi ne a samu dunkulewar Nijeriya ta hanyar ba da damar hada auratayya da ’yan kasuwa a tsakanin rarrabuwar kawuna don tabbatar da hadin kan kowa.
“Mun sami kyakkyawar tarba a nan. Ni ba sabo ba ne a nan domin an haife ni a Kano. Don haka na dawo gida.
“Don haka, an mayar da Firdaus ga mahaifinta. Ina ganin kaina a matsayin mahaifin ta don haka tana cikin kulawa. Kuma a Musulunci, aure amana ce da dole ne ka sadar da ita,” inji shi.
Shima da yake magana a madadin iyalan amaryar, yayan amaryar, Farooq Abdullahi Sarki Yola, ya ce Firdaus tana da suna da sauran kyawawan halaye yayin da ta girma a tsakanin fadar sarki da gidan Madakin Kano.
“Muna matukar farin ciki da alfahari da wannan auren. Ka san a rayuwa ba za ka iya hasashen inda za ka je ba, musamman aure.
“Aure zai iya kai ku ko’ina cikin duniya. Don haka dukkanmu ’yan Najeriya ne kuma dole ne mu rungumi juna mu dauki kanmu a matsayin iyali. Don haka muna mata fatan Alheri da kuma ango”.