An ga jinjirin watan Dhul Hijjah a kasar Saudiya inda Gobe Alhamis ya zama daya ga wata.
Hakan yanuna cewa, Za a gudanar da hawan Arfa kenan a ranar Juma’a 8 ga watan Yulin shekarar 2022, wanda kuma Ranar Sallah zai kama Asabar 9 ga watan Yuli.
Hukumomin kasar ne huka sanar da hakan a shafin suna facebook mai suna Haramain Sharafain.
Idan za’a iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, hukumomin saudiyya a jiya sun bada sanarwar fara duba jinjirin watan na Dhul Hijjah.
Sai dai a gefe guda har yanzu a Najeriya a na dakon sanarwar ganin watan na Dhul Hijjah da ga fadar mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar Na Uku.
A wani labarin na daban kuma.
Za Mu Tura Wakilai Birnin Landan Kan Tsare Ekweremadu Da Matarsa—- Majalissar Dattawa
Majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata ta bayyana cewa za ta tura wata tawaga mai karfi domin ganawa da Sanata Ike Ekweremadu a birnin Landan na kasar Birtaniya.
Idan za’a iya tunawa jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Ike Ekweremadu, wanda shine tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, an tsare shi ne tare da matarsa bisa zargin “cire sassan jiki wani yaro ” a kasar Ingila.
Majalisar ta yanke hukuncin ne bayan sun yi wata ganaawar sirri, na tsawon sa’o’i biyu a ranar Laraba.
Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Ahmad Ibrahim Lawan ne ya yabawa lauyoyin da suke kare Sanata Ekweremadu da matarsa, wadanda ya ce suna bakin kokarinsu wajen ganin an fitar da su daga komar rundunar yan sandan birtaniya.
Ya bayyana cewa ya gana da babban kwamishinan Biritaniya wanda ya yi masa bayani kan ci gaban shari’ar da kuma cikakken bayanin abin da ya faru.
Lawan ya kara da cewa tawagar majalisar dattawan za ta hada da mambobin kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje.
“Tawagar majalisar dattawan za ta hada da mambobin kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje wadanda za su yi tafiya nan da kwanaki biyu masu zuwa,” in ji Lawan