Wasu ‘yan bindiga sun shiga fadar Ikpomolokpo da ke unguwar Gege a karamar hukumar Ado a jihar Benue da sanyin safiyar ranar Litinin, inda suka kashe dan sarkin yayin da ‘suka yi Garkuwa da yarsa.
Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun afkawa al’ummar yankin ne da misalin karfe biyu na dare, inda suka nufi fadar shugaban kabilar Kuma suka yi mummunan barna.
Mazauna kauyen sun ce sun ji karar harbe-harbe da dama daga gidan hakimin, amma ba su iya shiga tsakani ba, saboda su kansu ba su da komai.
Shugaban karamar hukumar Ado, Cif James Oche, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a garin Makurdi Babban Birnin jihar, inda ya ce, an kira shi a kan lamarin.
“Wasu ‘yan bindiga da misalin karfe 2 na safiyar yau (Litinin) sun shiga gidan hakimin Ipomoloko ta katanga, inda suka nemi matar gidan, a wajan dan sarkin mai suna Thompson.”
“Saurayin ya shaida musu cewa bai san inda mahaifiyarsa take ba, sai suka harbe shi har lahira kuma yanzu suka tafi da ‘yar uwar,” inji shi.
Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa nan take ya sanar da dakarun Operation Whirl Stroke (OPWS) amma kafin su isa fadar, ‘yan bindigar sun tsere zuwa dajin Atiga da ke yankin.
Oche ya ce tuni sojojin suka fara bin sahun masu laifin da nufin cafke su da kuma kubutar da wanda aka sace.
Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar Benue, DSP Catherine Anene, har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a sameta ba ta wayar salula, saboda a kashe layin wayarta yake.
Comments 1