Shugaban kungiyar mabiya addinin kirista CAN Bishop Joseph Masin, reshen jihar Nassarawa ya samu rigar ‘yanci bayan da aka yi garkuwa da shi a satin da ya gabata.
An saki Bishop Masin ne da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar a garin lafia dake jihar ta Nassarawa, kuma ya samu damar kowama cikin iyalansa da misalin karfe 1:48 na dare.
Daya daga cikin ‘ya’yan Malamin fasto Sam Joseph ya tabbatarwa da manema labarai cewa malamin ya sami nasarar komawa cikin iyalansa.
Yaron ya kara da cewa, mahaifin nasa a halin yanzu yana bukatar hutu sakamakon wahalar da ya sha na yin tafiya mai nisan zango a kafa.
Yaron yace sun bada kudade domin sakin mahaifin nasu amma bai bayyanawa manema labarai ko nawa su suka biya ba.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-sanda-sun-kashe-masu-garkuwa-da-mutane-har-mutum-8-a-jihar-taraba-2/
Yaron yace an yi gaggauwar sakin mahaifin nasa ne sakamakon matsin-lamba da jami’an hukumar ‘yan sandasuka saka domin ganin an yi nasarar sakinsa.
Yayin da aka tuntubi jami’in hukumar ‘yan Sanda na Jihar Bola Longe, ya tabbatar da sakin shugaban kungiyar mabiya addinin kirista.
Longe ya bayyana cewa ba shi da masaniyar ko an biya wasu kudi domin sakin malamin, ya dai ce kawai jami’an hukumar na ta binciken ganin an sake sa.
Daga bangarensa kuwa, shugaban hukumar’yan sanda na jihar ya yu kira ga mutane da suke taimakawa jami’an hukumar da bayanai domin ganin an dakile muggan lafuka a jihar.