Jam’iyyar APC mai mulki ta umurci kungiyar lauyoyin ta da su nemi hakkinta kan sakamakon da kuma ayyana dan takarar gwamnan NNPP kuma zababben gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, Vanguard ta rawaito.
Kakakin jam’iyyar, Ahmed Aruwa ne ya bayyana hakan a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dan Takarar Gwamnan APC Ya Koka Kan Yadda Aka Kame Lauyoyinsa
A cewarsa, aikin bayyana hakan ya sabawa dokokin zabe da aka shimfida.
Ya ce, “Bayyana wanda ya lashe zaben kamar yadda INEC ta sanar ya saba wa tanadin dokokin da suka tsara yadda za a gudanar da zaben baki daya.
“Jam’iyyar APC ta Kano ta caccaki sakamakon da INEC ta bayyana, wanda ya tabbatar da dan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.
“Bayyana wanda ya lashe zaben kamar yadda INEC ta sanar ya saba wa tanadin dokokin da suka tsara yadda za a gudanar da zaben baki daya.”
Aruwa ya yi zargin cewa “INEC ta yi sabanin tanade-tanaden dokokin zabe inda ta ayyana Abba Gida Gida a matsayin wanda aka fi sani da shi zababben gwamnan jihar.”
Shugabancin jam’iyyar na jihar ya umarci lauyoyin ta da su ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar da ke zamanta a Miller Road Court Complex.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa wannan lamari dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Nasiru Gawuna ya taya zababben gwamnan murnar samun nasarar lashe zaben.
A wani labarin kuma, PDP Ta Yi Allah-Wadai Kan Kame Da Tsare Mambobinta A Jihar Kebbi
Jam’iyyar PDP a jihar Kebbi ta sake yin Allah-Wadai da abin da ta kira kame da tsare mambobinta da shugabannin jam’iyyar a kananan hukumomin Yauri, Kamba, Dandi, Kaniwa da Kalgo na jihar da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka yi, kamar yadda Nigerian Tribune ta rawaito.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa duk wannan cin zarafin da ake yi wa ‘ya’yanta duk wani yunkuri ne na hana su kin fitowa kada kuri’a a zaben da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.