Wasu da ake zargin bata gari ne sun kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke Iyana, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
DAILY POST ta ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kai kimanin takwas, sun haure katangar, inda suka shiga harabar kuma suka cinna wa ginin INEC wuta daga baya.
KARABTA WANNAN LABARIN: Zamfara: CP Kolo Ya Ziyarci Wasu Makarantu Tare Da Tabbatar Da Inganta Tsaron Su
An ce sun jika biredi da fetur sannan suka jefa guda cikin ginin ta kusurwoyi daban-daban don bankawa ofishin na INEC.wuta
Wakilin Majiyar Dimokuradiyya ya samu labarin cewa, jami’in tsaron da ke wurin, Azeez Hamzat, ya kirs ‘yan sanda da misalin karfe 1:00 na rana, inda ya ce ginin na ci da wuta.
Rundunar ‘yan sandan reshen Ibara ta ce ta tura jami’an tsaro zuwa wurin, tare da jami’an kashe gobara, domin kashe gobarar.
An tattaro cewa, ofishin jami’in mai kula da yiwa jama’a rijista da dakin taro ne gobarar ta shafa.
Hakazalika wata majiya ta shaida wa wakilin cewa gobarar ta shafa wasu kayayyaki.
“Babu wani rai da aka rasa kuma ba a samu rauni a gobarar ba” DAILY POST ta nakalto.
A WANI LABARIN KUMA: Jihar Nasarawa Ta Sami Sabon Kwamishinan Yan sanda
An tura sabon kwamishinan ‘yan sanda (CP), Maiyaki Muhammed-Baba, zuwa jihar Nasarawa.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Nansel Rahman, ya fitar, ya ce sabon Kwamiahinan ya karbi ragamar rugudanar ne daga hannun Mista Adesina Soyemi wanda a kwanan nan aka kara masa mukamin mataimakin sufeto Janar (AIG) na ‘yan sanda