Wani gini beni mai hawa bakwai da ake ginawa a kan titin Oba Idowu Oniru dake jihar Legas, ya ruguje inda mutane kusan shida suka makale.
Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojoji Ba Za Su Yi Kasa A Gwiwa Ba Wajen Tursasa Kungiyar IPOB – Nwachukwu
Ya ce an fara aiki a wurin domin ceto wadanda suka makale.
Ya ce, “Bayan isa wurin da lamarin ya faru, an gano wani gini mai hawa 7 da ba a kammala ba ya ruguje.”
Babu wani rauni da ya samu, sai dai an ce kimanin mutane shida ne suka makale a karkashin baraguzan ginin da ya ruguje.
“Za a bukaci na’urar tone baraguzan ginin da kayan aiki mai nauyi na hukumar domin ceto wadanda suka makale. Mun kunna shirin mayar da martani na jihar Legas Ana ci gaba da aiki.”
A wani labarin kuma, Hambararren Shugaban Sri Lanka Ya Koma Gida, Don Fuskantar Kiran Kama Shi
Hambarerren Shugaban kasar Sri Lanka, Gotabaya Rajapaksa, ya fuskanci kiraye-kirayen a kama shi a ranar Asabar bayan ya dawo gida daga gudun hijirar da ya yi da kansa karkashin kariyar gwamnatin magajinsa.
Rajapaksa ya tsere daga tsibirin karkashin rakiyar sojoji a watan Yuli bayan 1da dimbin jama’a suka mamaye gidansa na hukuma sakamakon zanga-zangar da aka shafe watanni ana yi biyo bayan rikicin tattalin arzikin da ba a taba ganin irinsa ba.