Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa filin wasa na Dan Anyiam domin taron gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC a jihar Imo. Kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Shugaban wanda ya isa filin wasan da misalin karfe 1:25 na rana, ya samu tarbar gwamna Hope Uzodimma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Duk Wanda Ya Hada Baki Da ‘Yan Siyasa, Zai Fuskanci Hukuncin Dauri – Kwamishinan INEC Yi Gargadi
Buhari ya kaddamar da titin MCC da Urratta mai tsawon kilomita 15 kafin ya nufi hanyar zuwa wurin taron gangamin.
Shugaban ya zarce kai tsaye zuwa wurin taron domin halartar gangamin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Shettima Kashim inda kuma za su yi jawabi ga dimbin jama’a.
A wani labari kuma, Buhari Ya Bukaci UAE Ta Janye Takunkumin Da Ta Sanya wa Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci dage takunkumin da gwamnatin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanya wa ‘yan Najeriya kan dokar hana biza.
A wata sanarwa da Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa ya fitar a ranar Talata, Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.