Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rantsar da Mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin sabon Alkalin Alkalan Najeriya (CJN) a yau.
Hakan ya biyo bayan murabus din da mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi ne saboda kalubalen koshin lafiya da yace yana fama da shi.
A halin yanzu dai mai shari’a Ariwoola shine babban alkalin kotun koli.
Kuma Ana sa ran za a rantsar da shi a yau da karfe 2 na rana kamar yadda majiya daga fadar shugaban kasar ta bayyana.
An haife shi a ranar 22 ga Agusta 1958, Mai shari’a Ariwoola ya kasance mai shari’a na Kotun daukaka kara kuma an daukaka shi zuwa benci na Kotun Koli.
A wani labarin kuma na daban.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fice daga kasar a safiyar yau Litinin zuwa kasar Faransa bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Tunde Rahman na ofishin yada labarai na Tinubu ya fitar ranar Litinin, ya ce shugaban nasa ya tafi birnin Paris na kasar Faransa domin gudanar da wasu muhimman taruka.
Ya lura cewa ana sa ran dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zai dawo kasar nan ba da jimawa ba ba tare da bayyana takamaiman ranar ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito tun da farko kafin tafiyar tasa, Tinubu ya halarci taron baje kolin wani littafi mai suna, ‘Mr. Speaker’ and launch of legislative mentoring initiative in commemoration of the 60th birthday of the Speaker of House Representatives, Femi Gbajabiamila, a Abuja ranar Lahadi.
Kana wani labarin ya bayyana cewa,
Mista Muhammad Tanko yayi murabus cikin gaggawa, a cewar majiyoyin kotun koli guda hudu da suka zanta da Jaridar Peoples Gazette a safiyar ranar Litinin.
Mai magana da yawun kotun kolin ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a safiyar ranar Litinin, amma ya ce za a yi karin bayani kan dalilinsa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito a makon da ya gabata daga zanga-zangar da alkalan kotun koli suka rubuta kan Mista Tanko, inda ake zarginsa da cin hanci da rashawa da rashin da’a da kuma rashin kula da jin dadin ma’aikata.
Zarge-zargen da ba a saba gani ba, masu sharhi na kotun suna kallon su a matsayin abin fashewa a tarihi, suna masu gargadin cewa hakan na iya dagula mata suna.
Mista Tanko ya amsa wa alkalan kotun, inda ya zarge su da rawa tsirara a kasuwa tare da wanke kansa daga aikata wani laifi.