Wani dan wasan kwallon kafa da ba a san ko wanene ba ya fadi ya mutu a lokacin da yake wasa a filin wasan kwallon kafa na Green Field, da ke unguwar Lekki a jihar Legas.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin tabbataccen shafin sa na Twitter a ranar Litinin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babban Ya Yan Gwamnan Bauchi Ya Rasu A Kasar Turkiyya
Daily Nageria ta ruwaito Mista Hundeyin ya ce jami’an ‘yan sanda reshen Maroko ne suka kawo bayanan a ranar Juma’a.
Ya kara da cewa dan wasan mai shekaru 31 da ba a san ko wane ne ba ya mutu da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar juma’a.
Kakakin rundunar yan sandan ya kuma ce an garzaya da shi asibitin Ever Care da ke Lekki domin yi masa magani inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.
“Bisa rahoton, tawagar jami’an tsaro sun ziyarci wurin wasan kwallon kafa da kuma asibitin da aka duba gawar tare da daukar hotuna.
“An ajiye gawar a dakin ajiyar gawa domin a tantance gawar. A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike,” inji shi.
Mista Hundeyin, ya shawarci jama’a, musamman ‘yan wasa, da kada su takurawa kansu yayin atisayi.
Ya kuma shawarci idan sun gaji su je waje su huta.
A WANI LABARIN KUMA: Mutum Uku Sun Mutu A Hatsarin Mota A Kaduna
Wani hatsari da ya rutsa da motar Toyota Corolla a ranar Litinin ya halaka mutum uku daga cikin fasinjoji shida da ke cikin motar bayan motar ta kwace daga hannun matukinta
Daily Post ta ruwaito cewa, motar tana kan hanyar zuwa Kachia ne a lokacin da a rasa yadda za ta yi, kuma ta ci karo da wani rami.