Jam’iyyar PDP a jihar Filato ta bayyana Musa Agah a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Agah zai taka takarar a inuwar jam’iyyar a zaben maye gurbi na mazabar Jos ta Arewa/Bassa.
Agah wanda shi ne kenneman maye gurbin mamba mai wakiltar mazabar Irigwe/Rukuba a majalisar dokokin jihar Filato a halin yanzu, ya samu kuri’u 152 inda ya doke abokin hamayyarsa Jonathan Dabo wanda ya samu kuri’u 127.
An shafe sa’o’i 5 ana gudanar da zaben ba tare da tangarda ba.
Da yake bayyana sakamakon zaben, shugaban kwamitin zaben, Mista Francis Orogu ya ce, “Hon. Musa Agah ya samu kuri’u 152, Jonathan Dabo ya samu kuri’u 127, David Racha ya samu kuri’u daya.
“Kamar yadda kuke gani, abin da ya faru a nan ya kasance a bayyane, mun ba da matakin wasa ga duk masu son tsayawa takara, kuma kuna iya ganin yadda komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Orogu ya kuma yaba da irin hadin kai da duk masu son tsayawa takara, sannan ya bukace su da su marawa jam’iyyar baya domin ganin ta samu nasara a zaben da za a yi a karo na biyu.
Da yake jawabi bayan lashe zaben fidda gwanin Agah, ya godewa wakilan da suka ba shi goyon baya.
“A gaskiya, ina godiya ga ’yan’uwana da suka fafata da ni, na yi imanin nasarar ta mu ce duka.