Wani fitaccen dan majalissar sarki a Najeriya, Alapinni na Oyoland, Babban Hakimi, Alh Abdul-Rasheed Shehu ya rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa, Alapinni na Oyo, wanda yana daya daga cikin Oyomesi (sarakunan da ke da alhakin zaben Alaafin na Oyo na gaba) ya rasu da sanyin safiyar Lahadi, 18 ga watan Satumba, 2022, bayan ya yi fama da rashin lafiya da ba a bayyana ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Tuni Tattalin Arzikin Najeriya Ya Durkushe Idan Ba Dan Bangaren Shari’a Ba — Malami
An tattaro cewa za a yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a yammacin yau a cikin gidan iyali.
Karamar hukumar Oyo ta Gabas ta tabbatar da rasuwar sarkin Yarbawa a cikin wata sanarwa da Azeez Ismail Arekemase, mai baiwa shugaban karamar hukumar shawara ta musamman kan harkokin yada labarai ya fitar.
A wani bangare na sanarwar na cewa; “Cikin zuciya amma tare da mika wuya ga ikon Allah, ma’aikatan karamar hukumar Oyo ta Gabas sun yi nadamar sanar da rasuwar babban sarki Alh.Abdul-Rasheed Shehu.. Alapinni na Oyo Land, da sanyin safiyar yau Lahadi 18 ga watan Satumba, 2022.”
“Za a yi jana’izarsa a gidansa yau da karfe 4:00 na yamma. Allah ya jikansa da Aljannar Firdausi Amin.”
An ce marigayi Alapinni na Oyo shi ne mahaifin Sarauniya Badira, wadda ta auri marigayi Oba Lamidi Adeyemi.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Oba Lamidi Adeyemi III bayan ya shafe shekaru 50 akan karagar mulki, ya rasu yana da shekaru 83 a duniya a ranar 23 ga watan Afrilu, 2022.
A wani labarin kuma, Zazzaɓin Lassa ya kashe mutane 171 a Najeriya – NCDC
Cibiyar Kula da Manyan Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta sake samun karin mutane takwas da suka kamu da cutar zazzabin Lassa da mutum daya tsakanin 5 zuwa 11 ga watan Satumba, 2022.
Hukumar NCDC ta shafinta na yanar gizo ta ce sabbin kwayoyin cutar sun kawo adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar zuwa 917 da 171, bi da bi.
Comments 1