Alhaji Isa Baba Buji, daya daga cikin wakilan jihar Jigawa a babban taron jam’iyyar APC na musamman da ke gudana a Abuja ya rasu.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Buji ya rasu a babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata.
Har zuwa rasuwarsa kwatsam, Buji ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai kula da jihar Jigawa ta kudu.
Rahotanni sun bayyana cewa, ya kwana da safe a ofishin hulda da jama’a na Kasa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, a lokacin da yake shirin zuwa wurin taron.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar APC reshen jihar Jigawa, Bashir Kundu, ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, “Tabbas ya rasu da safiyar yau”.
Jami’in hulda da jama’an ya kara da cewa “ya fadi a ofishin hulda da jama’a na jihar Jigawa da ke Abuja, inda aka garzaya da shi asibiti ya rasu kafin a isa asibitin. Da muka isa asibitin, an tabbatar da rasuwarsa.”
A wani labarin Kuma na daban.
Sa’o’i 3 da tsara fara taron fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyar APC, Amma harayanzu shiru kake ji
Har yanzu ba a fara gudanar da babban taron kasa da na fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki ba bayan sa’o’i uku.
Taron dai kamar yadda shirin ya nuna zai fara ne da misalin karfe 1:30 na rana a dandalin Eagle Square da ke Abuja inda gwamnonin APC da ‘yan majalisu suka iso.
Baya ga wakilan kasa daga wasu jihohi, jiga-jigan jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki, har yanzu ba su isa wurin da karfe 4:30 na yamma ba.
Wakilai daga Kaduna, Imo, Jigawa Gombe, Borno, Enugu, Edo, Benue, Bauchi suma basu iso ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto da karfe 4:30 na yamma.
Gwamnonin jam’iyyar APC, shugabannin majalisar wakilai na jihar da na Tarayya wakilai, da masu neman takarar shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da shugaban kasa Muhammadu Buhari, za su isa filin tsakanin karfe 1:30 na rana zuwa karfe 3:15 na rana, kamar yadda aka tsara abaya.
Sai dai daga Gwamna Atiku Bagudu, shugaban kungiyar gwamnonin na APC, da ‘yan majalisar dokokin kasa kadan, ne suka Isa wurin, yayin a wasu ba su iso ba.
An shirya cewa, za’a sa taken kasa don fara bude taron a hukumance da karfe 3:30 na rana. Sai dai har yanzu ba a fara gudanar da Taron ba da karfe 4:30 na yamma ba, lokacin da aka tsara cewa Gwamna Bagudu na jihar Kebbi, Kuma Shugaban gwamnonin jam’iyar APCn nakasa zai yi jawabi.