Jami’an hukumar EFCC ta cafke tsohon shugaban Yan majalisu, Abubakar Bukola Saraki, bisa zargin sa da almundahana. Kamar yadda Jaridar premium ta wallafa a shafinta
Abubakar Bukola Saraki, tsohon gwamnan Jahar Kwara, ya shiga hannun hukumar ne a ranar Asabar, wanda wannan ba karamin illa bace ga siyasar shi.
Bukola Saraki, a matsayin sa na tsohon shugaban Yan majalisu a tsakanin 2015 zuwa 2019, sau da dama ana tuhumarsa da laifin cin hanci da rashawa, da kuma mallakan kayayyaki da ba kan ka’ida ba, inda aka gurfananar dashi a babban Kotu a shekarar 2018.
KARANTA:- Tirkashi: Yan sanda a Kaduna sun cafke mutane 492 tare da kwato shanu 679
A dai wannan lokacin dai zai amsa tambayoyin a wajen hukumar EFCC bisa laifin almundahana da wasu kudade.
A wani labarin Manyan masu ba gwamna shawara sun koma APC
Manya-manyan masu baiwa gwamnan Jahar Taraba shawara Darius Ishaku, sun fice daga Jam’iyyar PDP sun koma jam’iyyar APC.
Mutane ukun sune Audu Ade, Francis Fidelis da Kyauta Shehu Lau. Gaba dayan su sun bar aikinsu.
Wannan ya biyo bayan sama da magoya bayan jam’iyyar ta PDP dubu hamsin da suka koma APC a yammacin jahar Taraba.
Shugaban jam’iyyar ta APC a Jahar Taraba Barista Ibrahim El-Sudi, yace jam’iyyar APC na samun karuwa kullun da kullun.
Ya cigaba da cewa Jam’iyyar APC ta shirya tsaf don cigaba da ayyukan da za su kara ciyar da jam’iyyar gaba.
Alhaji Saidu Usman Dakingari, shugaban kwamitin rikon kwarya, kuma tsohon gwamnan Jahar Taraba yace suna a cikin jahar suna kokarin gudanar da shirye-shirye na ciyar da Jam’iyyar gaba.
Yace muna kara baiwa magoya bayan Jam’iyyar APC hakuri da su cigaba da kasancewa tare da jam’iyyar.