- Hukumar EFCC ta tsare tsohuwar ministar harkokin mata da cigaban jama’a Pauline Tallen bisa zargin karkatar da kudade.
- Tsare ta ya biyo bayan zargin cin hanci da rashawa har naira biliyan biyu da hukumar take mata.
- Jami’an hukumar EFCC sun yi wa Tallen tambayoyi ne a hedikwatarta da ke Wuse, Abuja.
A halin yanzu tsohuwar ministar harkokin mata da ci gaban jama’a Pauline Tallen tana hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, bisa zargin karkatar da kudade.
Wasu majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin, sun tabbatar wa wakilinmu cewa jami’an hukumar EFCC sun yi wa Tallen tambayoyi ne a hedikwatarta da ke Wuse, Abuja.
KARANTA WANNAN: Rikicin PDP: Kotu Ta Tabbatar Da Korar Ayu Daga Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa
Ko da yake cikakkun bayanai kan zargin da ake yi wa tsohuwar ministar na kan zayyana, wata majiya mai tushe ta shaida wa jaridar PUNCH cewa ta yi iyaka ne da cin hanci da rashawa har naira biliyan biyu.
“Tsohuwar ministar ta isa ofishinmu na shiyyar Abuja (ba hedkwatarmu ba), bisa gayyatarta, da misalin karfe 12 na rana, amma har yanzu jami’an binciken hukumar na ci gaba da aiki har zuwa karfe 8:30 na dare.
“Ana bincikenta ne bisa zargin karkatar da kudade da kuma cin hanci da suka kai Naira Biliyan 2, kuma ana zargin an karkatar da wani bangare na kudin ne daga aikin wanzar da zaman lafiya na uwargidan shugaban kasa daga Afrika.”
Ba a samu mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
A wani labarin kuma, Murna Har Kunne: Dan Takarar Gwamnan NNPP da Wasu Mambobi 2000 Sun Koma APC
Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a jihar Ebonyi Adol-Awam da tulin mambobin jam’iyyar sum koma APC.
Daukar matakin sauya shekar zuwa jam’iyyar APC mai mulki ya biyo bayan dimbin rigingimun da suka dabaibaye jam’iyyar NNPP a jihar.
Adol-Awam yace zai cigaba da jajircewa wajen ganin an samar da ci gaba da shugabanci na gari domin amfanin kowa.