By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan ta’addan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne a ranar Alhamis sun harba makamin roka a yankin Gomari Ayafe mai tazarar mitoci 200 daga NAF Base dake Maiduguri.
Wakilin jaridar Blueprint ya tattaro cewa fashewar ta kashe mutum daya tare da jikkata wasu.
Har ya zuwa lokacin da ake cike hada wannan rahoto, ba a bayar da wani tabbaci a hukumance kan lamarin ba.