Daga: Abbas Yakubu Yaura
Fitacciyar Jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, Ada Ameh, ta rasu.
An tattaro cewa an garzaya da ita zuwa asibitin kamfanin man fetur na Najeriya NNPC amma ta rasu kafin su isa wurin.
Jarumar, wacce aka fi sani da rawar da ta taka a matsayin Emu a wasan kwaikwayo na iyali na African Magic, The Johnsons, ta rasu ne a daren ranar Lahadi.
Shugaban kungiyar ’yan wasan kwaikwayo ta Najeriya, Emeka Rolla, ya tabbatar wa da jaridar PUNCH rasuwar Jarumar ta wayar tarho da safiyar ranar Litinin.
A Wani Labarin Kuma Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta ce ta samu rahoton wasu tsofaffin mambobinta da suka koma jam’iyyar adawa ta PDP a jihar.
A cewar wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar na jihar, Kwamared Yusuf Idris Gusau, jam’iyyar APC ba ta san sun sauya sheka ba.
Ya ce sun gaza sanar da jam’iyyar a hukumance matakin da suka dauka wanda ba don wani dalili ba ne illa kawai girman kai.
“Masu goyon bayansu da na jam’iyyar sun ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar APC mai da hankali kan jama’a, don haka abin mamaki ne a ji suna ikirarin dubban mabiya.
“Kamar yadda suka bar jam’iyyar APC, muna farin ciki da cewa jam’iyya mai mulki ta ci gaba da karba tare da maraba da karin wadanda suka sauya sheka a jihar tare da sanya ta a gaban sauran jam’iyyun siyasa,” in ji shi.