By Ishaq Dabai
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya a mince da nadin Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir a matsayin sabon sarkin Gaya.
Da yake jawabi ga manema labarai a safiyar ranar Lahadi, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji yace nadin ya biyo bayan shawarwarin da masu zabar sarki a masarautar bayan bayar da sunayen ‘yan takara uku.
Usman Alhaji yace “Gwamnan jihar Kano tana da ikon da aka bata na Dokar Masarautar Kano 2020 kamar yadda aka gyara tace ta amince da nadin Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir a matsayin sarkin Gaya”.
Sabon sarkin ya gaji mahaifinsa marigayi Alhaji Ibrahim Abdulkadir wanda ya rasu ranar Laraba yana da shekara 91 a duniya
Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir shi ne Chiroman Gaya kafin nadinsa a matsayin sarkin Gaya.
Gwamna Ganduje ya taya sabon sarkin murna tare da yi masa fatan samun nasara bisa nadin da akayi masa.
Masarautar Gaya na daya daga cikin Masarautun da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro a shekarar 2020.