By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa biyo bayan tashi wata gobara ta lalata dukiyoyi da kadarori na miliyoyin naira a lokacin da gobarar ta tashi a mashigar ruwan Elechi dake unguwar Mile One a Diobu a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar inda tayi a sarar dukiya mai tarin yawa.
Kazalika Gobarar data tashi daga rukunin gidaje na a Shanty ta kai ga gine-gine, inda mazauna garin suka rasa abin da za su dauka daga tarkacen jirgin daya kama da wuta.
Akalla Sama da gidaje 100 ne abin ya shafa inda iyalai kusan 300 suka rasa matsugunansu a sakamakon tashin gobarar.