Jarirai 11 da aka haifa sun mutu sakamakon gobara da ta tashi a wani asibiti a birnin Tivaouane da ke yammacin kasar Senegal, in ji shugaban kasar .
Jarirai hudu da aka haifa a can ne suka mutu bayan da wata gobara ta tashi a dakin haihuwa na asibitin , magajin garin ya ce an samu matsalar wutar lantarki a sashin na’urar sanyaya iska na dakin haihuwa .
Har ila yau, iftila’in na ranar Laraba ya biyo bayan cece-ku-cen da kasar ta yi kan mutuwar wata mata mai suna Astou Sokhna , wadda ta rasu a lokacin da aka bayar da rahoton cewa tana rokon a yi mata tiyata a lokacin da ta shafe sa’o’i 20 tana nakuda .
Da yake tabbatar da barkewar gobarar a shafinsa na twitter, shugaba Macky Sall ya ce gobarar da ta tashi a asibitin Mame Abdou Aziz Sy Dabakh na sashen kula da masu haihuwa dake kasar ta Senegal.
Rahotannin na nuni da cewa gobarar ta tashi ne sakamakon wani tarstatsin wuta Lantarki a cikin asibitin kamar yadda yan siyasar kasar suka bayyana .
An ceto jarirai uku daga gobarar, inji magajin garin, Demba Diop Sy.
MR SLY ya shaidawa kafafen yada labarai na cikin gida cewa gobarar ta bazu cikin sauri kuma har yanzu jami’an agajin gaggawa na can a wurin domin kashe wutar .
Rahotanni daga kafafen yada labarai na kasar sun ce an kaddamar da sabon asibitin domin maye gurbin Wanda gobarar ta tashi.
Da yake mayar da martani game da wannan mummunan lamari , ministan lafiya , Abdoulaye Diouf Sarr , ya ce ana gudanar da bincike kuma zai dakatar da tafiyarsa da ya irya domin komawa kasar Senegal nan take .
Sai dai lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta kan halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a kasar .
Dan majalisar daga jam’iya Mai adawa a kasar Mamadou Lamine Diallo ya soki gwamnati inda ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa : ” jarirai da yawa sun Kone a wani asibitin gwamnati … Wannan ba abin da za’a lamunta ba ne ” .
A halin da ake ciki kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnati da ta kafa wani “kwamitin bincike mai zaman kansa don tantance alhaki da hukunta wadanda suka ke da hannu a sanadiyar tashin gobarar .”
Amnesty ta yi kira da a binciki dukkan asibitocin haihuwa na Senegal bayan wani abu makamancin haka ya afku a garin Linguère da ke arewacin kasar a bara .
Comments 1