Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, a ranar Alhamis ya nada ma’aikatan gwamnati 30 a matsayin mayan sakatarori.
Sunayen wadanda aka nada na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Dr Festus Oyebade.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Halastaccen Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Ogun
Sanarwar ta ce wadanda aka nada a matsayin PS za su cike guraben da ake da su a ma’aikatun gwamnati.
Wadanda aka nada sun hada da;
Injiya Kamoru A. Babalola; Injiniya S. O. Ajao; Mista M. A. K. Jimoh, Mista R. A. Popoola da kuma Dakta D. O. Ogunrinade: Madam J.K. Odediran.
Kazalika a kwai Mista Oyesiku Adelu; Malam Babajide Falade; Madam Funmilola Oyewole; Malam O.A. Ogundun; Mrs. Bukola Aderibigbe.
Sauran sun hada da Misis Taiwo Oladunjoye; Dakta A. A Oni; Malam Lekan Babalola; Madam Sola Akinsola; Malam K.N. Akintola; Mista J. S. Adekomi; Misis Jibola Falode.
Sannan akwai Mis AY Esan; Misis C O Falade; Mista C O Fasina; Misis Gbemisola Fayoyin; Mr MA Olawale; Mr SA Raji; Pharmacist Kunle Adebayo.
Akwai, Mr TO Akinwumi; Mr Richard Oyegbami; Mr Fatai Adekilekun; Malam M.O. Obidiya; Injiya |. A Babalola.
A wani labarin kuma, Alkalai 9 Sun Samu Sauyin Wajen Aiki A Jihar Kano
Babban Alƙalin Alƙalai na kotunan Shari’ar addinin Musulunci dake jihar Kano Dr. Tijjani Yusuf Yakasai, ya amince da sauyin wurin aiki da aka yiwa wasu Alkalan manyan kotunan shari’ar addinin Muslinci da kuma na kananan kotunan shari’ar Muslunci su 9.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takadda mai dauke da sa hannun Daraktan kotunan shari’ar addinin musulinci Muhd Aminu Ibrahim, wadda kakakin kotun shari’ar addinin musulinci na jahar Kano Muzammil Ado Fagge ya rabawa manema labarai a birnin Kano.
Sanarwar ta ce ”wadannan sauye sauye sun fara aiki ne nan ta ke, kuma ana umartar kowanne Alkali da ya hanzarta bin wannan umarni da zarar ya sadu da takaddar.