Gwamnatin jihar Kaduna ta garkame dukkannin Kasuwannin dake ci mako-mako a Kannanan hukumomi 5 dake jihar, tare da haramta Saida man Fetur a galan, a dukkannin kananan hukumomin.
Kwamishinan kula da harkokin cikin gida da al’amuran tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin, 30 ga watan Agustan shekarar 2021.
Inda sanarwar tace ” Biyo bayan dubi da hukumomin tsaro sukayi kan sha’anin tsaro a jihar, Gwamnatin Kaduna na sanar da al’uma dakatar da cin Kasuwannin mako-mako a kananan hukumomin; Birnin Gwari, Igabi, Giwa, Chikun, da kuma Kajuru, wanda zai fara aiki nan take.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Jirgin Saman soji Nigeria ya hallaka Yan bindiga da dama a Zamfara
“Gwamnatin ta kuma haramta Saida man Fetur a galan a ciki da wajan gidan Mai, a dukkannin kananan hukumomin da ka lissafa”
Kazalika Gwamnatin jihar Kaduna ta umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da al’uma sun bi wannan dokar sau da kafa.
Har’ila yau gwamnatin ta yi kira ga al’uma yankunan da lamarin ya shafa, da su bai wa Gwamnati goyan baya, a yunkurin ta na yaki da aiyukan yan bindiga a fadin jihar baki daya
Gwamnatin ta kuma ce, Kofa a bude take domin al’uma su bada bayanai da za su taimaka mata, wajan yakar yan bindiga ta wadannan lambobin wayar kamar haka:
09034000060
08170189999
Comments 1