By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar tabbatar da ingancin makarantu ta jihar Kaduna (NSSQA) a ranar Juma’a, ta rufe wasu makarantun Islamiyya biyu bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara shida fyade tare da yi wa wata ciki.
An rufe daya daga cikin Makarantun Madrasatul Ulumul Deeniya wa Tahfizul Qur’an dake Rigasa bisa zargin yi wa yarinya ‘yar shekara shida fyade a harabar makarantar.
Haka kuma sauran makarantar Islamiyya dake Tsohon Masallacin Juma’a dake Kachia, a karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, an rufe ta ne sakamakon zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 ciki da wani malami mai shekaru 50 yayi a makarantar.
Shugaban KSSQA, Mista Idris Aliyu, wanda ya rufe makarantar Islamiyya dake Rigasa, ya bayyana cewa an ci zarafin yarinyar ‘yar shekara shida a harabar makarantar, kuma hukumar makarantar ta rufe ta kuma ta yi ikirarin jahiltar lamarin.
Aliyu yace bayanan dake gaban ma’aikatar ilimi sun nuna cewa kakar wanda ta tsira ta je wurin hukumar makarantar ne ta shigar da kara amma dalibai da malaman Islamiyya sun lakada mata duka.
Sannan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya bayar da umarnin a rufe Islamiyya har sai an kammala bincike kuma a kama mai laifin.
“Shugaban makarantar zai dauki alhakin aikata wannan aika-aika har sai an bayyana sunayen duk mutanen dake cikin makarantar sannan kuma wanda ya tsira ya gano wanda ya aikata laifin kuma a hukunta shi,” in ji shi.
“Wadanda ke da alhakin cin zarafin kaka, musamman shugaban makarantar, za a kuma gurfanar dasu a gaban kuliya.”
“Wannan ya yi dai-dai da alhakin da gwamnatin jihar ke da shi na kare al’ummar da ba su da karfi a jihar,” inji shi.
Shugaban makarantar, Malam Kabir Abdullahi, ya musanta zargin, yana mai cewa “ba fyade ba ne.”Abin da muka tattara shi ne, wani yaro da ba a san ko wanene ba ya raunata yarinyar a al’aurarta da sanda,” in ji shi.
Abdullahi ya ce tuni jami’in dan sanda DPO, Rigasa, ASP Abubakar Bauranya, ya himmatu wajen gudanar da binciken lamarin.
DPO ya tabbatar da samun karar kuma ya yi daidai da labarin shugaban makarantar Islamiyya.
Sai dai kakar wadda ta tsira, Hajiya Batul Gambo ta dage cewa an ci zarafin jikarta, kuma an tabbatar da hakan ne daga Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Asibitin tunawa da Yusuf Dantsoho dake Tudun Wada, Kaduna.
Wani rahoton likita na Dakta A Raji ya sanya wa hannu ya tabbatar da ikirarin Gambo na cewa an yi wa yarinyar ‘yar shekara shida fyade.
Da yake tsokaci kan fyade da ciki da aka yi wa yarinyar ‘yar shekara 12 a Kachia, Aliyu ya ce wanda ya tsira tana da ciki wata shida.
Sannan ya bayyana cewa kwamishiniyar aiyuka da jin dadin jama’a, Hajiya Hafsat Baba da kwamishiniyar ilimi Hajiya Halima Lawal za su hada kai da ‘yan sanda domin gudanar da bincike tare da tabbatar da an yi adalci.
“A halin da ake ciki, makarantun biyu za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an kammala bincike kuma a gurfanar da wanda ya aikata laifin bisa tsarin doka,” in ji shi.