Kwamishinan ilimi na jihar, Shehu Makarfi, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wurin taron bita da kungiyar Marubutan a fannin Ilimi Zamani a Najeriya ta shirya.
A yau ranar Alhamis ce dai gwamnatin jihar , ta fitar da sabon jadawalin bude makarantun da ke jihar, tun bayan watanni da makarantun suka kwashe a rufe sakamakon hare-haren yan bindiga a jihar.
Taron bitar, wanda aka shirya a matsayin wani bangare na ayyukan ci gaba, don bikin ranar kare ilimi ta duniya daga harin, an Mai lakabi da; “Sakamakon hare -haren ta’addanci a kan Ilimi a Najeriya.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Mun fatattaki mayakan Tigray a Afra’ Inji Gwamnatin Kasar Habasha
A cewar Mista Makarfi, ana sa ran daliban jihar za su fara koma wa makarantu daga ranar Lahadi, 12 ga Satumba, shekarar 2021.
Kazalika kwamishinan ya ce, maimakon ci gaba da yin wa’adi na uku da aka soke a jihar, makarantun za su ci gaba da zangon farko na jadawalin karatun su na shekarar 2021/2022.
Ya kara da cewa, jihar ta fitar da dabaru don tabbatar da kammala wa’adin na uku ta hanyar Amfani da yanar gizo.
Ya ce za a ci gaba da komawa makarantun ne bi da bi.