By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta soke matakin da ta dauka na dakatar da kungiyoyin kwallon kwando ta Najeriya daga shiga dukkannin wasannin kasa da kasa.
Babban sakatare na dindindin na ma’aikatar matasa da wasanni Ismaila Abubakar ne ya bayyana haka yayin wani taro a Abuja ranar Alhamis, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jibia: NCS Ta Shawarci Al’ummomin Kan Iyaka Suyi Amfani Da Damar Yin Kasuwanci Don Bunkasa Tattalin Arziki
A cewar Abubakar, matakin na baya-bayan nan ya samo asali ne daga wata wasikar daukaka kara daga hukumar kwallon kwando ta Najeriya (NBBF), mai dauke da sa hannun Mista Musa Kida.
Ya ce shiga tsakani da masu ruwa da tsaki suka yi, da tsaffin ‘yan wasan kwallon kwando na Najeriya da kuma ‘yan Najeriya masu kishin Najeriya don neman mafita kan batutuwan ne ya jawo shawarar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da janyewar Najeriya daga dukkan wasannin kwallon kwando na duniya.
Sunday Dare, Ministan Matasa da Ci gaban Wasanni, wanda ya tabbatar da ci gaban ya ce dakatarwar za ta dauki tsawon shekaru biyu.
Ya ce ci gaban da aka samu zai baiwa gwamnati damar mayar da hankali kan kokarin da ake na sake fasalin wasanni.
Comments 1