Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bada umarnin rufe dukkannin manyan kasuwanni dake fadin jihar.
Gwamnan ya kuma bada umarnin rufe dukkannin gidajen Mai dake wasu kauyuka a jihar, inda kuma ya haramta Sai da man Fetur a cikin galan a jihar.
Ya yin da haryanzu, ba’a fayyace dalilin da yasa gwamnan ya bada wannan umarni ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun hallaka mutane 7, tare da jikkata wasu a Katsina
Kazalika hakan na zuwa ne sa’o’i kadan, bayan da daliban Makarantar Kwalejin Gona da kimiyar kiwon dabbomi dake Bakura a jihar ta Zamfara, suka shaki iskar yanci daga hannun yan bindiga.
An saki daliban ne a yau juma’a, tare taimakon wasu daga cikin yan bindigan da suka tuba, daga mummunan aikin.
A cewar Gwamnan jihar, an sako daliban ne, ba tare da biyan ko si-si ba, a matsayin kudin fansa ba.
Yes