Wani hari ta sama da sojojin Najeriya suka kai kan ‘yan bindiga ya kashe kananan yara bakwai tare da raunata wasu biyar bisa kuskure a Nijar, kamar yadda wani gwamnan yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a yau Lahadi.
“An samu kuskure da hare-haren da Najeriya ta kai kan iyakar kasar da ta yi sanadin mutuwar mutane a yankinmu a kauyen Nachade” a ranar Juma’a, in ji Chaibou Aboubacar, gwamnan yankin Maradi.
“Wadanda abin ya rutsa da su yara 12 ne, bakwai daga cikinsu sun mutu, biyar kuma suka jikkata.” inji shi.
Akwai Karin bayani……..
Awani labarin Kuma na daban.
Jakadan Kenya a Najeriya Ya yanke Jiki ya Fadi Abuja, Inda ya ce Ga Garinku nan
Babban kwamishinan Kenya a Najeriya, Wilfred Machage, ya fadi ya mutu a Abuja.
Machage mai shekaru 65, an ce ya yanke Jiki ya fadi ne a gidansa da ke Abuja ranar Asabar, inda aka garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Ma’aikatar harkokin wajen ta kasar Kenya ta fitar da wata sanarwa inda ta sanar da rasuwar Machage.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yin nadamar sanar da rasuwar Honarabul Dr. Ambasada Wilfred Machage, babban kwamishinan Kenya a Najeriya, wanda ya rasu a yau (Asabar).
“Jakada Machage ya fadi ne a gida kuma ya mutu a asibiti jim kadan bayan haka da misalin karfe 12:30 na sanyin safiyar yau (Asabar) a Abuja babban Birnin Najeriya. Matarsa na tare da shi a lokacin da wannan abin takaici ya faru.”
Sospeter Magita, dan uwansa wanda tsohon jakadan Kenya ne a Rasha, ya shaidawa jaridar The Standard cewa ya rasu ne bayan ya ci abincin rana.
Sanarwar ta kara da cewa “Lokaci ne mai matukar bakin ciki da a yau na rasa babban aminina kuma amintaccena.”
An ce matar marigayi babban kwamishinan tana tare da shi lokacin da ya fadi.
Ya kasance Sanata a majalisar dokokin Kenya tsakanin shekarar 2013 zuwa 2017 kafin a nada shi a matsayin babban kwamishinan Najeriya a watan Janairun shekarar 2018.