Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa NECO, ta sanar da fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Nuwamba/Disambar shekarar 2022, SSCE.
Magatakardar NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Minna, jihar Neja, ya ce mutane 59,124 ne suka zana jarrabawar, maza 31,316, wanda ke wakiltar kashi 52.96, yayin da dubu 27,808, wanda ke wakiltar kashi 47.03 cikin 100 mata ne.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗumi-Dumi: Buhari Ya Tsawaita Wa’din Amfani da Tsohuwar N200
Wushishi ya kara da cewa, adadin wadanda suka zana harshen turanci sun kai 58,012, daga cikinsu 44,162, wanda ke wakiltar kashi 76.13 cikin 100 sun samu kiredit da sama da haka, yayin da adadin wadanda suka zana ilmin lissafi ya kai 57,700, daga cikinsu 43,096, wanda ke wakiltar kashi 74.69 bisa dari sun samu credit da sama da haka.
Ya kuma bayyana cewa adadin wadanda suka samu credit biyar zuwa sama sun hada da Ingilishi da lissafi sun kai 33,914 wanda ke wakiltar kashi 57.36 cikin dari.
“Haka zalika 46,825 ‘yan takara, masu wakiltar kashi 79.20% sun samu maki biyar (5) da sama da haka ba tare da la’akari da harshen Ingilishi da lissafi ba,” in ji shi.
Dangane da matsalar rashin gudanar da jarabawa, ya ce an yiwa mutane 11,419 katin shaidar cin zarafi daban-daban, sabanin 4,454 a shekarar 2021, lamarin da ke nuna yadda ake samun karuwar matsalar.
A cewarsa, hakan ya faru ne saboda ingantuwar dabaru da jami’an sa ido suka dauka.
“Hakan ya kai ga sanya sunayen manyan jami’ai hudu (4) daya (1) kowanne daga cikin jihohin Rivers da Plateau da biyu (2) daga jihar Ogun saboda ba da taimako da kuma rashin kulawa,” inji shi.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa NECO ta gudanar da jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2022, SSCE, daga ranar 21 ga watan Nuwamba zuwa 21 ga watan Disambar shekarar 2022. An fitar da sakamakon bayan kwanaki 57.
A wani labarin kuma, Obaseki Ya Ba Da Umarnin Kamo Tsohon Gwamna Oshiomhole Kan Wani Rikici
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya bayar da umarnin tsare tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole, bisa zarginsa da hannu a wata zanga-zangar da ta kai ga lalata bankuna da kuma mutuwar kimanin mutane uku a jihar.
A wata sanarwa da kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a na jihar, Chris Nehikhare, ya fitar a ranar Laraba, Obaseki ya yi zargin cewa Oshimohole ya hada ‘yan baranda domin lalata bankuna tare da kawo cikas ga zaman lafiyar jihar saboda karancin kudin naira.