Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro, Janar Lucky Irabor; Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, da sauran hafsoshin tsaro a halin yanzu suna ganawar sirri a hedikwatar rundunar da ke Abuja.
Taron ake ci gaba da yi na daga cikin kokarin da shugabannin jami’an tsaro ke yi na kubutar da fasinjojin jirgin kasa da Akayi Garkuwa da su a hanyar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wata guda da ya gabata.
Wata majiya ta shaida wa jaridar Daily Truat cewa, an matsa wa jami’an tsaro matsin lamba wajen ganin an kubutar da wadanda ake tsare da su kafin Idin Sallah ko kuma babban kwamandan sojojin kasar ya sanya musu takunkumi.
Majiyar ta kara da cewa taron zai kuma kunshi tsare-tsaren zabe mai zuwa duba da sanarwar da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi na cewa ‘yan ta’adda na shirin jefa bama-bamai a wuraren ibada da wuraren taruwar jama’a.
“Abin da na sani shi ne hukumomin tsaro suna taro don kubutar da wadanda harin jirgin kasan Kaduna ya rutsa da su. Ina nufin wadanda ‘yan ta’adda suka yi Garkuwa da su, Mai yiwuwa ma a yi la’akari da batun tsaro a babban zabe mai zuwa,” inji majiyar.
Wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya wanda ya kasance a wurin taron ya lura da wani haske a kan hanyar da ke zagaye da Asokoro zuwa Sakatariyar Gwamnatin Tarayya.
Daily trust ta ruwaito cewa a ranar Larabar da ta gabata ne ‘yan ta’addan suka fitar da hotunan wadanda suka yi garkuwa da su su 62 wadanda suka hadar da maza 17 da mata da kananan yara a cikin hotuna daban-daban.
A wani labarin Kuma na daban.
Yanzu-Yanzu: Kotu ta tabbatar da Sagagi a matsayin shugaban PDP a Kano
Wata Babbar Kotun Taraiya a Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyar PDP na jiha da ƙananan hukumomi 44 ƙarƙashin shugabancin Shehu Sagagi har sai ta gama sauraren ƙarar da ke gaban ta.
Da ya ke ƙwarya-ƙwaryar hukunci a kan ƙarar, alƙalin kotun, Mai Shari’a Taiwo O. Taiwo ya tabbatar wa da duk wasu roko da shugabancin Sagagi ya shigar gaban sa.
Taiwo ya kuma gargaɗi uwar jam’iyar ta ƙasa da ƙasa ta sake ta ɗauki wani mataki a kan shugabancin na Sagagi.
A tuna cewa a ranar 29 ga watan Maris ne dai Taiwo ya bada umarnin dakatar da jami’ar daga rushe shugabancin Sagagi da kuma kafa kwamitin riƙo a jihar har sai ta gama sauraron ƙarar baki ɗaya.
Amma sai uwar jam’iyar ta yi kunnen kashi ta rushe shugabancin jam’iyar, sannan ta kafa kwamiti na mutum 7 domin ya rike jam’iyar.
Daga nan kuma sai Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ki amincewa da kwamitin rikon kwaryar a wani mataki na yin biyayya ga kotun.