Hukumar Jami’ar Legas ta yanke shawarar duk Dalibai subar dakin kwanan su na Makaranta nan take.
Daya daga cikin Mahukunta a Jami’ar wanda bai bari a ambaci sunan sa ba, ya shaidawa Jaridar Premium time cewa an yanke wannan hukuncin ne duba da karuwar cutar Covid-19 a makarantar.
KARANTA:- Aminu Waziri Tambuwal ya sha alwashin kara himma wajan tabbatar da lafiya a Jahar Sokoto
A zaman da mahukunta makarantar suka gabatar a yau Laraba, sun yanke wannan hukuncin saboda dawowar cutar Covid-19 karo na uku da kuma matsalar da cutar ka iya haifarwa, suka yanke dukkan daliban subar dakin kwanan su, Kamar yadda ya bayyana.
A rahotan da daya daga cikin maaikacin mu ya kawo muku a baya, ya ruwaito cewar
Akwai yiwuwar Kulle Dakunan Dalibai a Jami’ar UNILAG sakamakon cutar Covid-19 kashi na uku
Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya
Akwai yiwuwar Majalisar Gudanarwar Jami’ar Lagos, ta kulle Dakunan Daliabai, bayan ta kammala taron Gaggawa data ke yi a yau Laraba, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
Wani ya bayyana cewa, an Kira taron ne domin daukar mataki sakamakon cutar Covid-19 datake yawaita a Makarantar.
“Taron ba dadewa zaiyi ba. zamu tattauna ne akan ko mu kulle Dakunan Dalibai, idan za’a cigaba da karatu a Makarantun. wasu daliban na barin Dakunan Daliban tun kafin mu dauki mataki” inji wani Malami.
Wakilin Jaridar Punch ta bayyana cewa, ana tunanin taron zai Fara da Karfe 2 na rana a yau a Dakin taro na J.F Ade Ajayi.
Ana cigaba da zaman dar-dar a tsakanin Dalibai da Malamai, a yayinda ake cigaba da samun yawaitar masu kamuwa da cutar a Makarantar, inda wasu Daliban da Ma’aikata sun kamu da cutar.
Mai Magana da Yawun Makarantar Nonye Oguama yace, bazaiyi magana ba a lokacin da aka tuntube shi.
Daya daga cikin Daliban dake Kwana a Dakunan Dalibai a cikin Jami’ar, yace ” Muna da mutane da dama Wanda suke fama da rashin lafiya Wanda kuma yana tattare da alamomin cutar. Bamu San mike faruwa ba. Dole mu tafi gida maimakon zama a Makaranta.”
Wata Daliba ta tabbatar dacewa, an gwada abokiyar ta an kuma tabbatar tana dauke da cutar, Wanda tuni an killace ta.
Haka Zalika, Majalisar Gudanarwar Jami’ar Lagos ta tabbatar dacewa Cibiyarta ta kula da Lafiya, tace an samu karuwar masu kamuwa da cutar Covid-19 a Makarantar.
Ta kuma tabbatar dacewa, Makarantar tana fuskantar Kashi na 3 na cutar Covid-19.