Jam’iyyar PDP ta tsayar da Sanata Philip Aduda a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa.
Haka kuma an zabi Sanata Chukwuka Utazi (Enugu ta Arewa) a matsayin sabon mai tsawatarwa na marasa rinjaye a majalissar.
Nadin na kunshe ne a wata wasika mai dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Samuel Anyawu.
Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar a farkon zaman majalisar.
Nadin Aduda ya biyo bayan murabus din tsohon shugaban marasa rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe (Abia ta Kudu).
Abaribe, a makon da ya gabata, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party zuwa All Progressives Grand Alliance (APGA).
Har ila yau, jam’iyyar PDP a cikin wasikar da ta aike wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ta bayyana cewa Sanata Utazi ya nada shi a matsayin sabon mai tsawatarwa na marasa rinjaye, sakamakon daukakar da Sanata Aduda ya yi a matsayin shugaban marasa rinjaye.