Allah yayi wa jarumin kannywood na cikin shirin kwana casa’in Alhaji Umaru Malumfashi wanda aka fi sani da “KAFI GWAMNA” rasuwa.
Bayanan rasuwar tasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daya daga cikin jaruman masana’antar ta kannywood Abba El-Mustapha ya fitar ta kafar sada zumunta ta Instagram a daren yau Talata 27 ga watan Satumba 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani Na PDP a Jihar Ogun, Ta Umarci a Sake Sabo
Duk da cewa jarumin Abba El-Mustapha bai yi cikakken Bayanin dalilin rasuwar sa ba har zuwa lokacin hada wannan Rahoto.
Sannan ya bayyana cewa “Za’a yi Jana’izarsa a gobe Laraba a unguwar Hotoro dake jihar Kano da karfe 9 na safe.”
Kazalika ya kara da cewa “Muna Addu’ar Allah Ya jikansa ya gafarta masa kurakuransa yasa Aljanna ce makomarsa. Idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani.”
Kafi gwamna kafin rasuwar dai ya kasance tsohon jami’in Hukumar Custom, kuma ya na daya daga cikin dattawan masana’antar kannywood.
A wani labarin kuma, Gwamna Wike Ya Dawo Da Jirgin Jihar Rivers Da Aka Yi Watsi Da Shi A Jamus
Wani jirgin sama Legacy 600 mallakar jihar Rivers da ake zargin gwamnatin da ta shude ta yi watsi da shi a cikin wani yanayi da ba a sani ba, an kwato shi kuma aka dawo dashi Rivers.
Gwamna Nyesom Wike a lokacin da yake karbar jirgin da aka yi jigilar sa zuwa filin jirgin sama na Fatakwal, Omagwa, a karamar hukumar Ikwerre, ranar Talata, ya ce gwamnatinsa ba ta wasa da kananan siyasa wajen dawo da jirgin.