Jirgin yaki mai lamba A-29 wanda Najeriya ta sayo daga Amerika ya sauka a Najeriya.
Ofishin masu watsa labarai ta hukumar tsaro suka fidda hakan. Amman kawo yanzu ba’a fidda labarin a gwamnatance ba. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa
Da yiwuwar masu kera Jiragen sun cika alkwarin samar da Jiragen yaki 6 a cikin sha biyu a wannan watan da Kasar Najeriya zata sayo.
KARANTA:- Babbar magan: An kulle Jami’ar Bayelsa har sai mama ta gani
A watan May ne, Kamfanin kera Jiragen na EDSI dake Amerika suka sanar da hukumar Najeriya kan tafiyar aikin.
Lokacin da Konel Authur Ford, Jami’in Kasar America ke zantawa da NASS cewa yayi, “10 daga cikin Jirage 12 suna gaf da kammala.”
Sauran biyun kuma za’a musu tsari ne kawai wanda ya shafi nau’in salon aikin sojan sama.
Ford yace shida daga cikin Jirage 12 zasu sauka a Najeriya cikin watan July, sauran kuma zasu kammala kamin karshen watan Satumba.
Jami’an sunce, “Jiragen za su taimaka matuka wajan shawo kan matsalar tsaro a kasar nan.”
Tun a watan Mach ne, shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace shida daga cikin Jirage 12 zasu sauka a Najeriya.
Sannan an tura Mutane 14 don koyo tukin Jirgi a kasar Georgia.