Daga: Abbas Yakubu Yaura
Rahotannin da ke isowa daga garin Iseyin a jihar Oyo na nuni da cewa sarki Aseyin na Iseyin ya kwanta dama.
Sarkin wanda ya jima yana kwance a asibiti, rahotanni sun bayyana cewa ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi a Asibitin Kwalejin Jami’ar (UCH) Ibadan.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/ganduje-ya-raba-tallafin-naira-miliyan-3-8-ga-iyalan-wadanda-suka-rasu-a-hadarin-mota/
Gobe da safe za a dauke gawarsa daga asibiti zuwa garin kamar yadda majiyoyi a garin suka bayyana.
Wani tsohon dan majalisar dokokin jihar, dan asalin Iseyin, wanda ya zanta da Jaridar DAILY POST ya tabbatar da rasuwar sarkin.
Tsohon dan majalisar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Na kira wasu ne da na ji labarin da safe.”
“Daga baya sun tabbatar min da hakan da yammacin yau Lahadi”
“Aseyin ya mutu. Gobe da safe za a dauke gawarsa daga asibiti”.
Idan zaku tuna cewa sarakunan gargajiya akalla bakwai ne suka kwanta dama a cikin watanni tara da suka gabata a jihar Oyo.
Shahararren cikin sarakunan gargajiya shine Soun of Ogbomoso, Oba Jimoh Oyewumi wanda ya rasu a ranar 12 ga watan Disambar shekrar 2021.
Oba Saliu Akanmu Adetunji, tsohon Olubadan ya rasu a ranar 2 ga watan Janairun wannan shekarar.
Alaafin 45 na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi shi ma ya rasu a watan Afrilun bana.
A Wani Labarin Kuma Jami’an ‘yan sandan da ke aiki a sashen Iju,a jihar Legas sun cafke wasu jami’an sojojin bogi hudu.
An kama sojojin na jabu ne a wata mota kirar Mazda ranar Lahadi 24 ga watan Yuli da misalin karfe 1:30 na rana a unguwar Iju da ke Legas.
Wadanda ake zargin sun hada da Samuel Abel mai shekaru ‘28, Victor ljeemai 35, Lukman Salabiu 43 da Oyinyechi Macus mai shekaru 30.
A cafke sune yayin wani sintiri na yau da kullun karkashin jagorancin CSP Gbenga Stephen, jami’in ‘yan sanda na sashen Iju.
Da yake tabbatar da kamun, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an mika wadanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na Yaba dake jihar domin ci gaba da bincike.”
Idan zaku iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa makonni biyu da suka gabata jami’an ‘yan sandan da ke aiki da sashin Orile sun kama wani sojan bogi a hanyar Sari-iganmu, Orile.