Cocin Katolika ta Ondo ta bayyana cewa za a gudanar da jana’izar jama’ar da harin ta’addancin da aka kai cocin St. Francis Catholic Church a garin Owo, na jihar Ondo ya shafa ne, a ranar Juma’a 17 ga watan Yuni, 2022.
A cewar cocin, mutane 40 ne suka mutu a harin, yayin da wasu da dama suka jikkata.
A ranar Litinin, Daraktan Sadarwa na cocin Diocese na Ondo, Rabaran . Augustine Ikwu, ya tabbatarwa jaridar Daily Post labarin
Ya bayahna cewa, Jana’izar jama’a, a cewar daraktan, za a yi shi ne a wata sabuwar makabarta dake kan titin Emure a garin Owo.
Ya zuwa yanzu adadin wadanda suka rasu ya kai 40, wadanda suka jikkata na ci gaba da karbar kulawa a cibiyar kula da marasa lafiya ta tarayya da kuma cocin St. Louis Catholic da ke Owo da kuma wasu asibitoci masu zaman kansu a jihar.
Sai dia bayan kimanin mako guda da faruwar lamarin, babu wanda aka kama dangane da harin.