Wata kotun laifuffuka ta musamman da ke zamanta a Ikeja jihar Legas, ta yanke wa John Abebe, surukin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari, Daily Trust ta rawaito.
An yanke wa Abebe hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari tare da zabin biyan tarar Naira miliyan N50m a cikin kwanaki 30.
KARANTA WANNAN LABARIN: Canjin Kudi: Idan har halastaccen kuɗi ne da kai, ka kai shi CBN – Bashir Ahmad ga Ganduje
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da Abebe, wanda kanin uwargidan tsohon shugaban kasa, Stella Obasanjo ne a gaban kuliya, bisa zarginsa da yin jabun takardu.
An gurfanar da Abebe ne bisa tuhume-tuhume hudu a gaban kotun manyan laifuka ta jihar Legas da ke Ikeja.
EFCC, a cikin tuhume-tuhumen, ta yi iƙirarin cewa Abebe “yana sane ya ƙirƙiri” wata takarda a ranar 30 ga watan Nuwambar shekarar 1995 da BP Exploration Nigeria Limited ga Inducon (Nigeria) Ltd ya rubuta.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi ikirarin cewa dan kasuwan ya “saka ba bisa ka’ida ba” a shafi na 2 na wasiƙar da aka ce “bayani mai zuwa: “Haka kuma a lura cewa ‘Zabin Saye’ ya shafi matakin farko na NPIA ne kawai. Sayayya ta dala miliyan 4 don haka bai da nasaba da samar da mai a kowane filinmu.”
A cewar EFCC, Mista Abebe ya kuma yi yunkurin “karkatar da tsarin shari’a” ta hanyar gabatar da wasikar da ake zargin an yi masa na jabun takardu a ranar 30 ga watan Nuwambar shekarar 1995 “a matsayin shedar karya” a kotu, a kara mai lamba FHC/L/CS/224/2010. tsakanin Dakta John Abebe, Inducon Nigeria Limited da Statoil Nigeria Limited.
An gurfanar da shi ne a kan tuhume-tuhume hudu.
Mai shari’a Mojisola Dada ta yanke hukuncin ne bayan da aka tabbatar da cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da hakan ba tare da wata shakka ba.
Mai gabatar da kara karkashin jagorancin Mista Rotimi Oyedepo SAN ta gurfanar da wanda ake tuhumar ne a ranar 26 ga watan Yulin 2018 bisa tuhume-tuhume uku da suka shafi halasta kudi da kuma jabun takardu.
A wani labarin kuma, Ba zan iya yiwa Tinubu aiki ba bayan sakamakon zaben Ekiti – Segun Oni
Tsohon gwamnan Ekiti, Segun Oni ya musanta yin aiki da Bola Tinubu, ɗan takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa a karshen mako ta mai magana da yawunsa, Jackson Adebayo.