Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jos, babban birnin jihar Filato, ta yanke wa tsohuwar ministar albarkatun ruwa, Misis Sarah Ochekpe, hukuncin daurin watanni uku a gidan yari.
Kotun ta kuma yankewa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Raymond Dabo, da Evangelist Leo Sunday Jitung hukuncin daurin watanni uku a gidan yari su ma.
Mai shari’a Musa Kurna ne ya yanke hukuncin a ranar Talata.
Jaridar DAILYPOST ta ruwaito cewa mutanen ukun sun shafe shekaru hudu ana shari’a bisa tuhumar su da suka shafi hada baki da kuma karkatar da kudade.
Sai dai hukuncin yana da zabin tarar Naira miliyan daya.
A wani labarin Kuma na daban.
Kasar Syria a ranar Talata ta bayyana cewa tana goyon bayan matakin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin na amincewa da jamhuriyar Ukraine guda biyu da suka balle a matsayin masu cin gashin kansu.
Faisal Mikdad ya ce “Syriya na goyon bayan shawarar da shugaba Putin ya yanke na amincewa da jamhuriyar Luhansk da Donetsk kuma za ta ba su hadin kai.”
Kamfanin dillancin labaran kasar Syria ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Faisal Mikdad yana fadar haka a taron Valdai Forum da ke birnin Moscow a jiya Talata.
“Abin da kasashen Yamma ke yi a kan Rasha a yau ya yi daidai da abin da suka yi wa Siriya a lokacin yakin ta’addanci,” in ji shi.
Kasar Rasha dai ita ce babbar kawar shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad tun bayan barkewar yakin kasar Siriya a shekara ta 2011.
A jiya litinin, Putin ya sanar da shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnati Olaf Scholz na Jamus a wata tattaunawa ta wayar tarho game da matakin da ya dauka na rattaba hannu kan takardar amincewa da ‘yancin cin gashin kai na jamhuriyar biyu masu goyon bayan Rasha.
Jamhuriyoyin biyu masu goyon bayan Rasha sun hada da yankin gabashin Ukraine da ake kira yankin Donbas.
Mikdad ya ce, Amurka da kasashen yammacin duniya na ci gaba da taimakawa ta’addanci a kasar Siriya, wanda ke barazana ga yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya.
dpa