Alamu na nuna cewa matsalar samar da wutar lantarki a kasar na na iya kara kamari daga ranar Laraba, yayin da kungiyar kwadago ta umarci ma’aikata a bangaren wutar lantarki da su sassauta gudanar da ayyukan su, tare da fara yajin aikin sai baba ta gani, kan al’amuran ma’aikata da ke da alaka da kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa wato TCN.
A karkashin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa, NUEE, kuma a matsayin share fagen yajin aikin, ma’aikatan da suka gamu da su ka fusata na shirin karbe iko da babban ofishin Kamfanin TCN na kasa da ke babban birnin Tarayya Abuja a ranar Talata.
Da Yuwuwar Diago Dalot Ya Koma Barcelona Yayin Da Aubameyang Zai Tafi United
A wata takardar da Babban Sakataren Kungiyar NUEE, Joe Ajaero ya fitar, mai taken “Kiran daukar Mataki”, zuwa ga manyan mataimakan sakatarori da sakatarorin tsare-tsaren shiyya-shiyya mai kwanan wata 15 ga watan Agusta, 2022, kungiyar ta umurce mambobinta da su tabbatar sjn bi umarninta kamar yadda ta tsara.
Akwai karin bayani……..
A wani labarin kuma na daban.
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 300 da kayayyakin abinci a Sokoto
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 350 da kayan abinci a wasu unguwanni uku da ke karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.
Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Abubakar Ghani, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutane da dama sun rasa matsuguni a yankin.
Ya ce lamarin ya faru ne a karshen mako, inda ya ce kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Shiyar Ajiya, Makers da kuma Runji.
Mai baiwa gwamna shawara na musamman Aminu Tambuwal wanda shine shugaban hukumar Alhaji Zabairu Magaji yace gidaje 250 ne suka lalata a kauyukan uku.
Ya yi nuni da cewa, ba a samu asarar rai ba a lokacin ifti’la’in amma ambaliyar ruwan ta tafi da kayan abinci da dama.
Ya jajanta wa al’ummar yankin tare da ba su tabbacin gwamnatin jihar za ta samar musu da kayayyakin agaji cikin gaggawa.
Mataimakin shugaban karamar hukumar, Ibrahim Lawal, ya yabawa gwamnatin jihar kan yadda ta gano mutanen da lamarin ya shafa a cikin kankanin lokaci.
Ya kuma yi kira da a samar da kayan agaji a kan lokaci ga wadanda abin ya shafa, inda kuma ya kara da cewa, da yawa daga cikinsu sun rasa matsuguni ba tare da abincin da za su ci ba.