By Abbas Yakubu Yaura
Wata mata kuma Sanata mai ci, Aishatu Binani, ta zama ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Adamawa.
Sanata Binani mai wakiltar Adamawa ta tsakiya ta fafata da maza biyar ne inda ta lashe tikitin jam’iyyar a zaben fidda gwani na gwamna da aka kammala a jihar.
Ta samu kuri’u 430 inda ta kayar da babban abokin hamayyarta kuma tsohon shugaban hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Nuhu Ribadu, wanda ya samu kuri’u 288.
Tsohon gwamnan jihar, Jibrilla Bindo, ya samu kuri’u 103.
DUBA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Gwamnan Kaduna a Jam’iyyar APC
A yanzu dai Binani ta zama mace ta farko da ta lashe takarar kujerar gwamna a wata babbar jam’iyyar siyasa a jihar.
A wani labarin kuma Sanata Uba Sani ya Lashe Zaɓen Fidda na Gwamnan Kaduna a Jam’iyyar APC
Jami’in zaben fidda gwani Anachuna Henry ya bayyana cewa Uba Sani ne ya lashe zaben fidda gwani a safiyar Juma’a.
Yace an yi wa wakilai 1,275 rajista, sai 1,245, sula sami karbuwa, a yayinda wakilai 1,235 suka kada ƙuri’a, sai Ƙuri’a 1,196 ta zama halastacciya, sai Ƙuri’u 39 aka ƙi amince wa dasu.
Henry ya bayyana cewa Uba Sani ya samu ƙuri’u 1,149 inda ya doke sauran ‘yan takara biyu, Bashir Abubakar da ya sami 37, sai Kuma Sani Sha’aban wanda ya samu kuri’u 10.
A jawabinsa bayan ayyana shi, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa nasarar da ya samu ita ce nasarar kowane dan jam’iyyar, inda ya ce “Wannan ita ce nasarar ku. Wannan shine lokacin ku. Wannan shi ne farkon tafiya na ƙarfafawa da ci gaba.
A cewar sa, “Za mu ɗora kan kyawawan abubuwan da shugaban mu, Gwamna Nasir El-Rufa’i yayi tare da samar da haɗin kai a tsakanin jama’armu.
“Zaben fidda gwanin takarar gwamna na yau shiri ne na ban mamaki, nuna ladabi, hakuri da da’a daga wakilai. Mun nuna cewa mun yi imani da dimokuradiyya kuma a shirye muke mu bi bin doka da oda. Dimokuradiyya itace samun ƴan ci.
“Da zarar an bar mutane su bayyana ‘yancinsu na son rai, tsari da sakamako abin kyan gani ne.”
Ya kuma mika godiyarsa ga abokan takararsa, Alhaji Mohammed Sani Sha’aban da Alhaji Bashir Abubakar bisa yadda suka yi imani da tsarin dimokuradiyya inda ya ce, “Zan tuntubi wadannan manyan ‘yan siyasa da dabaru, in mika musu hannu na zumunci.
“Zan yi matukar godiya idan suka haɗa hannu da ni don kai jihar Kaduna zuwa ga matakin tudu.”
Comments 1