‘Yan majalisar dokokin jihar Neja sun tsige shugaban masu rinjaye, mataimakin shugaban masu rinjaye da kuma bulaliyar majalissar dokokin jihar, kamar yadda Jaridar The Nation ta rawaito.
‘Yan majalisar kuma sun zabi wadanda za su gaje su nan take.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu Kowa So Yake In Tsaya Takara A 2024 — Donald Trump
Wadanda aka tsige sune shugaban masu rinjaye, Saleh Ibrahim; Mataimakiyar shugabar masu rinjaye Binta Mamman da bulaliyar majalissar Bello Ahmed
An maye gurbinsu da Mohammed Abba Bala, wanda shi ne sabon shugaban masu rinjaye; Madaki Malik Bosso a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye da Salihu Tama Edati sabon shugaban bulaliyar majalissar.
A wani labarin kuma, Wata Ƴar Ƙaramar Yarinya Data Shafe Watanni 3, Ta Mutu Bayan Kwanaki 5 Da Sakin Ta
Yaro da aka saki bayan watanni uku a tsare ya mutu bayan kwana biyar
Wata ƙaramar yarinya mai suna Ewhalshoh Mandela Mairabo, wadda aka yi garkuwa da ita tare da mahaifiyarta da wasu 29, ta rasu kwanaki biyar bayan an sako ta.