Daga: Abbas Yakubu Yaura
Malaman kwalejojin ilimi a karkashin kungiyar ma’aikatan kwalejin ilimi (COEASU) ta dakatar da yajin aikin da ta tsunduma na watanni biyu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Laraba, 10 ga watan Agusta, 2022, bayan taron majalisar zartarwa na kasa da ta gudanar a dakin taro na Ukeje da ke ginin NCCE a Abuja, kamar yadda Jaridar Intelregion ta rawaito
KARANTA WANNAN LABARIN: Harin Cocin Owo: Sojoji, SSS sun kama wasu mutane 2 da ake zargi a Kogi
Idan za a iya tunawa, a ranar Talata, 14 ga watan Yuni, 2022, kungiyar ta fara yajin aikin na wata daya, tare da daukar wasu karin makonni uku, kan gazawar gwamnatin tarayya na sake kafa tawagar da za ta sasanta da kungiyar ta COEASU da gwamnatin tarayyar Najeriya a shekarar 2010.
Har ila yau, rashin fitar da farfado da asusai na Naira biliyan 15 da gwamnati ta yi da kuma dagewa kan tsarin biyan albashi da ma’aikata (IPPIS) da kuma adawa da tsarin (UTAS) ne bukatun kungiyar.
Sai dai a sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Larabar da ta gabata, ta ce matakin nata na dakatar da yajin aikin ya biyo bayan matakin da gwamnatin tarayya ta nuna a shirye take kan amsa bukatunta na kashi 95%.
Sanarwar ta ce; Mambobin Majalisar za su iya tuna cewa Sashen mu ya shiga yajin aikin gama gari na shekarar 2018 da aka dakatar a ranar 14 ga watan Yuni 2022 domin biyan bukatun kungiyar. Yajin aikin na kasa ya biyo bayan gazawar gwamnati (Tarayya dana Jihohi) wajen magance matsalolin da ke ci gaba da yaduwa tsakanin Gwamnati da kungiyar mu.
“An yada shawarar kungiyar ne a cikin wata sanarwar da ta fito daga taron majalisar zartarwa ta kasa COEASU (NEC) da aka gudanar a ranar 10 ga watan Yuni 2022 a Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta Asaba dake Jihar Delta.
“Ta wannan sanarwar, an sanar da Majalisa cewa NEC ta yi taro a yau 10 ga watan Agusta, 2022 a wurin
Zauren taro na Ukeje da ke ginin NCCE a Abuja, ya yi nazari sosai tare da duba nasarorin da aka samu kawo yanzu tun bayan ayyana yajin aikin.
“Binciken nasarorin da aka samu ya nuna gwamnati ta nuna fahimta da jajircewa kan kashi 95% na bukatun kungiyar don haka hukumar ta kasa baki daya ta amince da dakatar da yajin aikin na tsawon kwanaki sittin (60) masu zuwa.
“Don haka ana kira ga ‘yan majalisar da su koma bakin aiki tun daga ranar Alhamis
11 ga watan Agusta 2022. CEC ta yaba wa mambobin saboda goyon baya, hadin kai da fahimtar juna da suka nuna a yayin yajin aikin,” in ji sanarwar.