Manya-manyan masu baiwa gwamnan Jahar Taraba shawara Darius Ishaku, sun fice daga Jam’iyyar PDP sun koma jam’iyyar APC. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Mutane ukun sune Audu Ade, Francis Fidelis da Kyauta Shehu Lau. Gaba dayan su sun bar aikinsu.
Wannan ya biyo bayan sama da magoya bayan jam’iyyar ta PDP dubu hamsin da suka koma APC a yammacin jahar Taraba.
KARANTA:- Yau Yan fim za su gudanar da Zanga–Zangar, kin jinin Sahara Reporters
Shugaban jam’iyyar ta APC a Jahar Taraba Barista Ibrahim El-Sudi, yace jam’iyyar APC na samun karuwa kullun da kullun.
Ya cigaba da cewa Jam’iyyar APC ta shirya tsaf don cigaba da ayyukan da za su kara ciyar da jam’iyyar gaba.
KARANTA:- Gwamnatin Tarayya ta ce Nigeria na gabda kaddamar da tsarin 5G a Kasar
Alhaji Saidu Usman Dakingari, shugaban kwamitin rikon kwarya, kuma tsohon gwamnan Jahar Taraba yace suna a cikin jahar suna kokarin gudanar da shirye-shirye na ciyar da Jam’iyyar gaba.
Yace muna kara baiwa magoya bayan Jam’iyyar APC hakuri da su cigaba da kasancewa tare da jam’iyyar.
A wani labarin
Birtaniya za ta taimakawa Najeriya wajan yaki da ta’addanci
Ministan Birtaniya Boris Johnson, ya ce gwamnatin Kasar sa ta shirya tsaf don tallafawa kasar Najeriya kan matsalar tsaro.
Kamar yadda wani jawabi da mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya bayyana, Ministan Birtaniya Boris Johnson ya ce muna shirye a koda yaushe don tallafawa harkokin tsaro a kasar Najeriya, bayan ya gama sauraran shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Shuwagabanni biyu sun amince da tabbatar da hukuncin adalci wajan yaki da Kungiyoyin Yan ta’adda daban-daban dake Najeriya.
An dai samu wannan matsayar ne lokacin da ake gudanar da wani babban taro a kasar Birtaniya.
Shuwagabanni biyu sun ce yana da matukar amfani yin adalci wajan yaki da Yan ta’addan koda suwaye aka kama da sa hannunsu.
Haka kuma, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyanawa Ministan Birtaniya Boris Johnson kan irin nasarorin da ya samu a jagorancin kasar Najeriya, musamman wajan tsaron kayan abinci.
Shuwagabanni biyu sun kara tattaunawa kan yadda za su cigaba da habbaka harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu, da samar da wutar sola da kuma sauran abubuwan cigaban kasa.