Wata kungiyar farar hula a jihar Edo, Edo Civil Society Group karkashin jagorancin Kwamared Agho Omobude a ranar Talatar ta tare babbar kofar shiga babban bankin Najeriya da ke birnin Benin, sakamakon karancin kudaden Naira da ya janyo wa miliyoyin ‘yan Najeriya wahala.
Sakamakon zanga-zangar ya tilastawa motocin da suka bi titin Ring Road ta Akpakpava sauya hanya zuwa ta titin Igun -Sokponba kafin su hade da titin Ring Road.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Zamfara ta gargadi CBN, Bankuna kan sabbin takardun kudi
Masu zanga-zangar sun yi kira ga hukumar da ta dace da ta samar da sabbin takardun Naira domin rage radadin da ‘yan Najeriya ke fama da su a halin yanzu don samun kudadensu, yayin da suka bukaci CBN da ya fara bayar da takardun kudi na N100, N50 da N20 idan sabbin takardun sun yi karanci.
Omobude ya ce manufar musanya naira a wannan lokaci wani yunkuri ne da gangan da gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emiefele, da hadin gwiwar gwamnatin tarayya ke yi na sanya talakawa cikin wahala.
Ya kuma sha alwashin cewa kungiyar za ta ci gaba da zama a kofar bankin har sai shugaban babban bankin reshen Benin ya fito ya yi musu jawabi kan halin da ake ciki.
Ya kara da cewa rashin mutuntaka ne a ci gaba da barin ‘yan Najeriya su ci gaba da kasancewa cikin wannan wahala.
Omobude ya shaida wa The PUNCH cewa CBN a Edo da kuma kungiyar farar hula sun cimma wasu yarjejeniyoyin kafin su (masu zaman kansu ) su bar kofar bankin da misalin karfe 1 na rana.
A wani labarin kuma, Jam’iyar PDP Ta Bukaci Goyon Bayan Yan jarida
Dan takarar gwamnan jihar Delta a karkashin jam’iyyar PDP, Sheriff Oborevwori, ya nemi hadin kan ‘yan jarida domin tabbatar da burin mataimakin dan takaran shugaban kasa na Jam’iyar Dokta Arthur Ifeanyi Okowa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Dan majalisar ya yi magana ne a lokacin da ya jawabi a cikin shirin a shirin “Platform”, wani shiri da kungiyar NUJ reshen jihar Delta a Asaba ta shirya domin yiwa yan takara tambayoyi kan manufofin su.