Shugaban ‘yan ta’adda, Abdulkarim Faca-faca, wanda ake zargin yana cikin wadanda suka shirya harin da aka kaiwa ayarin motocin shugaban kasa Muhammadu Buhari a Katsina a lokacin da ya shirya hutun Sallar da ta gabata, an kashe shi tare da wasu ‘yan kungiyar sa guda takwas.
Rahotanni sun ce an kashe Faca-faca ne a ranar Asabar din nan a wani hari da rundunar sojojin saman Najeriya ta kai ta sama lokacin da suka kai sumame a wasu wuraren zama na ‘yan ta’adda a kauyen Marina da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina.
A cewar wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta, baya ga wadanda aka kashe, da yawa daga cikin ‘yan ta’addan sun samu raunukan bindigogi, duk da cewa sun samu tserewa. Ya kuma yi zargin cewa an lalata musu dukkan shanun da suka sato.
Da yake tabbatar da rahoton ga jaridar Vanguard, Honarabul Abduljalal Haruna Runka, dan majalisa mai wakiltar Safana a majalisar dokokin jihar Katsina ya ce.
“Gaskiya ne. Da yammacin ranar Asabar ne sojojin saman Najeriya suka kai sumame yankin inda suka ci gaba da aikin kawar da bata gari a safiyar yau. An kashe Abdulkarim Faca-faca da yaransa takwas a harin. An binne su ne a Marina, garinsu da safiyar ranar Lahadin nan,” inji Runka.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/wike-ya-yi-gargadi-game-da-zargin-daukar-yan-daba-don-zaben-2023/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Hakazalika rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta samu nasarar kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su bayan sun kai sumame a maboyar ‘yan ta’adda a kauyen Tandama da ke karamar hukumar Danja ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadin nan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ranar Asabar 6/08/2022, da misalin karfe 0530 na safe, bisa sahihin bayanan sirri, rundunar ta kai farmaki maboyar ‘yan ta’adda a Unguwar Dako, a kauyen Tandama, a karamar hukumar Danja, inda ta yi nasarar ceto wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su.
“Wadanda aka ceto sune: Alhaji Garba Danmallam mai shekaru 52, Unguwar Nuhu, karamar hukumar Danja, Rabiu Idris mai shekaru 45, na wannan adireshi, Abba Samaila mai sjekaru 38, mai wannan a direshi daya da su, Yunusa Sani mai shekaru 54, a kauyen Layin Sani, da ke Kafur.
Ishaq Yakub mai shekaru 40, na wannan adireshi daya, da Danjuma Samaila mai shekaru 45, na wannan duk masu adireshi guda
”
(SOLACEBASE)