Daga: Abbas Yakubu Yaura
Kamfanin jiragen sama na cikin gida na Najeriya, Azman Air, ya koma aiki bayan sabunta lasisinsa da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA tayi.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Kamfanin jirgin ya sabunta lasisin zirga-zirgar jiragen saman bayan dakatar da aikinsa a ranar Alhamis, da Hukumar NCAA ta yi, biyo bayan karewar wa’adin takardarsa, ciki har da rashin biyan bashi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-yanzu: NCAA Ta Dakatar Da Ayyukan Kamfanin Jiragen Sama Na Azman
Takardar da ke tabbatar da sabunta biyan lasisin Azman Air ta karanta cewa, “NCAA/ATR1/ATL118 yana aiki na tsawon shekaru biyar daga 2027 zuwa 2022 kafin a sake sa ran sake sabuntawa.”
An tattaro cewa kamfanin ya kuma mika fom din biyan haraji da na tsaro ga hukumar ta NCAA tare da sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ta Naira miliyan 50 duk wata domin biyan bashin da ya bari.
An dakatar da kamfanin na Azman Air ne watanni biyu bayan dakatar da kamfanonin jiragen sama na Aero Contractors da Dana Air, lamarin da ke nuni da rikicin da ake fuskanta a fannin sufurin jiragen sama.
Darakta Janar na Hukumar NCAA, Kyaftin Musa Nuhu, ya tabbatar a ranar Alhamis cewa hukumar na rike da lasisin sufurin jiragen sama na Azman Air har sai ya samar da takardun da ake bukata don sabunta lasisin gudanar da ayyukansa tare da sanya hannu kan wata yarjejeniya kan yadda za ta biya bashin da ta bari, da aka tara daga tarin Cajin Sabis na Fasinja.
A cewar Nuhu, Azman Air dole ne ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar ta MOU domin tattaunawa akan yadda ake biyan bashin da ke cikin Naira biliyan 42 da dala miliyan $7.8m na PSC, sannan kuma ya samar da Tax Clearance a matsayin daya daga cikin takardun ATL dinsa.
Majiyoyi sun yi ikirarin cewa kamfanin na Azman Air ya ci bashin har Naira biliyan 1.2bn na bashin da ya tara daga karbar kudin hidimar fasinja.
Nuhu ya ce da zarar kamfanin ya amince da hakan, zai samu amincewar sa domin kuwa hakan na daga cikin hanyoyin sabunta tsarin don tabbatar da cewa hukumar ba ta yi aiki ba.
A wani labarin kuma, INEC Za Ta Dauki Ma’aikatan Wucin Gadi Miliyan 1.4 Don Gudanar Da Zaben 2023 – Yakubu
LAGOS – Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa za ta dauki ma’aikatan wucin gadi miliyan 1.4 domin gudanar da babban zaben 2023.
Shugaban hukumar na kasa Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga kungiyar editocin Najeriya, jiya, a Legas.