Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya janye daga takarar shugaban kasa.
Obi wanda ya zagaya kasar domin neman goyon bayan wakilai a zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya janye kasa da sa’o’i 72 a fafatawar.
Obi ya rubutawa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, domin ya sanar da shi matakin da ya dauka na ficewa daga jam’iyyar adawa.
A cikin wasikar mai suna “Jam’iyyar PDP da ficewana daga takarar shugaban kasa,” Obi bai bayyana dalilin daukar matakin ba.
Da yake tsokaci game da wannan lamarin, Doyin Okupe, Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben Peter Obi, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su karaya domin tsohon gwamnan Anambra zai kasance a zaben shugaban kasa a 2023.